A yayin ganawarsu, Shugaba Geingob ya ce, kasarsa na shirya aiwatar da shiri guda goma na yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tsara domin raya tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar Namibia, don haka, kasarsa na maraba da kasar Sin ta zuba jari, domin taimaka mata wajen inganta harkokin masana'antu da ayyukan noma, samar da karin guraban aikin yi, ta yadda za a iya cimma moriyar juna.
A nasa bangare, Mr Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan yin hadin gwiwa da kasar Namibia wajen gudanar da shiri goma na hadin gwiwar Sin da Afirka yadda ya kamata, ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu gaba bisa zumuncin gargajiya dake tsakaninmu, da kuma yin hadin gwiwa a fannonin samar da ababen more rayuwa, kawar da talauci da dai sauransu, domin cimma burinmu na samun ci gaba tare. (Maryam)