in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar BRICS
2015-09-30 16:24:41 cri
An gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar BRICS a cibiyar MDD dake birnin New York a ranar Talata 29 ga wata, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron tare da yin jawabi mai taken "kara yin imani, da kara yin hadin gwiwa, da kuma kirkiro kyakkyawar makoma".

Wang Yi ya yi nuni da cewa, da farko, ya kamata kasashen membobin kungiyar BRICS su kara yin mu'amala da fadi ra'ayinsu na bai daya kan batun tsaron siyasar kasa da kasa. Na biyu, kasashen kungiyar su kara yin hadin gwiwa da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki. Sannan na uku, kasashen kungiyar su hada kai da taka muhimmiyar rawa kan batun samun bunkasuwa. Na hudu, kasashen kungiyar su inganta hadin gwiwarsu a fannoni daban daban. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China