Kamfanin dillancin labarai na kasar Syria SANA ya sanar a jiya Lahadi cewa, hare-haren bama-bamai da suka abku a garin Sayyidah Zaynab da ke wajen birnin Damascus, hedkwatar mulkin kasar Syria sun haddasa mutuwar mutane 83 yayin da wasu 178 suka jikkata.
wasu shaidun gani da ido sun gaya wa 'yan jarida cewar, da misalin karfe hudu na yammacin jiya Lahadi ne aka ta da wasu boma-boman da aka dana cikin wata mota a cikin garin, sannan bayan mintoci biyar, wasu 'yan kunar bakin wake biyu suka tayar da bam din dake daure a jikunansu, lamarin da ya haddasa mutuwa tare da jikkatar dimbin masu aikin ceto.
Haka zalika, kamfanin dillancin labarai na SANA ya bayyana cewa, a safiyar wancan rana kuma, wasu bama-bamai sun fashe a jere a unguwar Zahra a birnin Homs da ke tsakiyar kasar Syria, inda mutane 39 suka bakunci lahira, yayin da wasu fiye da dari suka ji raunuka.
Kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi ta sanar da daukar alhakin wadannan hare-hare a shafinta na sada zumunta. (Kande Gao)