Ministocin harkokin wajen Rasha da Amurka sun cimma daidaito kan abubuwan dake cikin yarjejeniyar wucin gadi ta tsagaita bude wuta a Syria
A jiya ne ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry suka bugawa juna waya sau uku, inda suka cimma daidaito kan abubuwan dake kunshe cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta wucin gadi tsakanin bangarorin Syria. Koda ya ke ba a cimma yarjejeniyar ba har yanzu saboda bangarori daban daban suna tattauna tare da kara shigar da wasu abubuwa a cikin yarjejeniyar.
A wani rahoto da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar a shafinta na intanet a wannan rana, an bayyana cewa, yarjejeniyar wucin gadin ba ta shafi matakan yaki da ta'addanci da kwamitin sulhun MDD ya amince da su ba. (Zainab)