Sanarwar kwamitin sulhun ta kuma nuna goyon baya ga kokarin da manzon musaman na babban sakataren MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya yi, kana ya jadadda bukatar aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron ministocin harkokin waje karo na 4 na kasashen da ke goyon bayan Syria da kuma kudurorin da kwamitin sulhun ya tsaida da sauransu.
Bugu da kari, kwamitin sulhun ya yi kira ga kungiyoyi daban daban na kasar Syria da su baiwa hukumomin jin kai damar kaiwa ga 'yan kasar Syria da ke matukar bukatar agaji, musamman ga jama'ar da ke yankunan da rikice-rikice ya rutsa da su
A ranar 3 ga watan 25 ga watan Fabrairu ne ake saran gudanar da sabon zagayen tattaunawar zaman lafiya game da kasar ta Syria da aka dakatar a ranar 3 ga watan Fabarairu a birnin Geneva. (Zainab)