Mataimakin wakilin dindindin na kasar Rasha dake MDD Mista Vladimir Safronkov ya bayyana cewa, manufar daftarin da Rasha ta gabatarwa kwamitin sulhun shi ne neman a mutunta 'yanci da cikakken yankin kasar Syria, da kuma yin watsi da duk wani mataki na kai hari kan Syria wanda zai kawo illa ga shirin warware matsalar kasar a siyasance da ake yi.
A saboda haka, Rasha tana fatan bangarori daban-daban da su gabatar da shawarwari game da wannan daftarin.
Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Syria Faysal Mekdad ya bayyana a jiya cewa, gwamnatin kasarsa a shirye take ta tunkari duk wani harin da aka kai mata. Kuma ya nemi kasar Turkiya da ta dakatar da harba rokoki a arewacin kasarsa, sannan ta daina kai hari a kasar ta kasa, ta kuma dakatar da baiwa masu fafutuka dake kasar Syria taimako. Shi ma Mista Mekdad ya bayyana takaicinsa game da matakin da kwamitin sulhun ya dauka na kin goyon bayan shirin daftarin da Rasha ta gabatar. (Amina)