Shugaban kwamitin sulhu a wannan wata, kana zaunannen wakilin Venezuela a MDD, Rafael Ramirez Carreno ya bayyana wa kafofin yada labaru bayan taron cewa, membobin kwamitin sulhu sun yi shawarwari kan daftarin kudurin Rasha.
Bangarori daban daban sun bayyana ra'ayinsu, amma ba su cimma matsaya daya kan wannan batu ba. Kwamitin sulhu yana share fagen sake yin shawarwari a kai a ranar Litinin mai zuwa.
Mataimakin zaunannen wakilin Rasha a MDD, Vladimir Safronkov ya bayyana wa 'yan jarida cewa, a cikin daftarin kudurin da Rasha ta rarraba wa membobin kwamitin sulhu, an yi kira da a girmama ikon mallakar kasa da ikon mallakar cikkaken yankin kasa ta Syria, da yin watsi da ko wane irin shiri na kai hari kan Syria ko kuma dasa shinge ga yunkurin daidaita batun Syria ta hanyar siyasa. Rasha ta yi maraba da bangarori daban daban na kwamitin sulhu da su gabatar da shawararsu yadda ya kamata.
Bayan taron kuma, zaunannen wakilin Turkiya a MDD, Yasar Halit Cevik ya bayyana cewa, Turkiya ta nuna goyon baya ga daidaita batun Syria a siyasance. Kafin wannan kuma, sau da yawa ne Turkiya ta bayyana cewa, ba za ta tura sojoji zuwa Syria da kanta ba, sai dai ta sami iznin kwamitin sulhun MDD, ko amincewar hadaddiyar kungiyar duniya ta yaki da kungiyar IS. Za ta dauki matakai tare da sauran kasashen duniya baki daya.(Fatima)