in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Syria ya nemi tattaunawar sulhu kan rikicin kasar ba tare da sharruda ba
2016-02-17 11:06:24 cri

Kamfanin dillancin labaran SANA, ya rawaito ministan harkokin wajen Syria Walid al-Moallem ya fada cewar, gwamnatin kasar a shirye take ta shiga tattaunawar sulhu da bangarorin 'yan adawar kasar ba tare da gindaya wasu sharruda ba.

Da yake jawabi a yayin ganawa da Staffan De Mistura, wakilin MDD kan rikicin Syria, Mr. al-Moallem ya bayyana cewar hukumomin Syria su kadai ne ke da alhakin yin nazari dangane da makomar kasar ba tare da fuskantar matsin lamba daga kasashen waje ba.

Wannan jawabi ya zo ne wasu 'yan makonni bayan tattaunawar sulhun da aka shirya da bangaren 'yan hamayyar a Geneva ta rushe, sai dai gwamnatin na zargin bangaren 'yan adawar da yunkurin wargaza shiri tattaunawar sakamakon sharrudan da ta gindaya.

An sake sanya ranar 25 ga watan Fabrairu domin tattaunawar, kuma kalaman al-Moallem sun nuna cewar, gwamnatin Syria a shirye take ta shiga tattaunawar sulhu kan rikicin kasar.

A wani labarin kuma, al-Moallem ya bayyana cewar gwamnatin Syria ta yi na'am da yunkurin De Mistura na shigar da kayayyakin tallafi ga al'ummar dake bukatar dauki, sai dai ya bayyana cewar wannan yunkuri ba shi da alaka da batun tattaunawar sulhun ta Geneva.

Al-Moallem ya sake jaddada bukatar kasashen yammacin duniya da su dage takunkumin da aka azawa kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China