Mista Cameron ya bayyana hakan ne bayan kammala taron majalisar ministocin kasar a wannan rana, ya kuma shedawa manema labaru cewa, gwamnati za ta shirya yadda jama'arta za su yarda da ci gaba da kasancewar Burtaniya cikin EU, a cewarsa, matakin da zai taimakawa Birtaniya wajen samun karin zaman lafiya, karfi da wadata saboda ganin kwaskwarima da EU ta yi, idan ba haka ba, barin EU zai jefa Birtaniya cikin mawuyacin hali na koma bayan tattalin arziki da rashin tsaro.
A gobe ne ake saran Mista Cameron zai gabatar da jawabi a majalisar dokokin kasar don kaddamar da shirin kuri'ar jin ra'ayin jama'ar.
Bayan da aka shafe kwanaki biyu ana kokarin cimma matsaya a taron kolin na EU, a karshe Mista Cameron da sauran shugabannin EU sun kai ga cimma matsaya daya don biyan wasu bukatun Birtaniya, ciki hadda rage tallafin da ake baiwa 'yan cin rani a Birtaniya, rashin shiga shirin karin dunkulewar Turai, da kuma matakan da suka shafi ba da kariya ga kasashen da ba sa amfani da kudin Euro da sauransu. Duk da hakan, 'yan kasar Birtaniya na bayyana fatansu matuka na ganin kasar ta janye daga EU. (Amina)