Kungiyar kasashen tarayyar Turai EU ta kira wani taron ministocin mambobi kasashenta a ran 14 ga wata, inda suka kai ga cimma matsaya daya wajen tsugunar da kaurar da 'yan gudun hijira dubu 40 dake shiga Italiya da Girka.
Mista Jean Aselborn, mataimakin firaminista kuma ministan harkokin waje na kasar Luxembourg, kasar dake rike da shugabancin karba-karba na EU a wannan karo, ya sanar da cewa, wannan kuduri na da wata ma'anar siyasa sosai, za a tattauna batun kan yadda za a tsugunar da 'yan gudun hijira bisa wannan tushe.
Wannan kuduri ya shafi 'yan gudun hijira da suka ketara zuwa kasashen Italiya da Girka daga ran 15 ga watan Agusta na shekarar 2015 zuwa ran 16 ga watan Satumba na shekarar 2016, amma EU ba ta kayyade adadin da kowace mambarta za ta karba ba.
Wani labarin kuma ya nuna cewa, EU za ta baiwa mambobinta dake shiga wannan aiki kudin tallafi, kuma kowanensu zai samu kudin Euro 6000 idan har sun karbi wani dan gudun hijira. (Amina)