Kwamitin kungiyar EU ya yi cikakken taro a jiya Laraba, inda a karo na farko ne da aka tattauna kan matsayin tattalin arziki irin na kasuwanci na kasar Sin. Kwamitin na tantance wannan batu daga dukkan fannoni, kuma zai ba da shawararsa a hukunce a kan wannan batu, wadda kasashe membobin kwamitin za su tattauna domin zartas da shi.
Mataimakin shugaban kwamitin kungiyar EU Frans Timmermans ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, matsayin da tattalin arzikin Sin ya dauka na da nasaba sosai tare da bunkasuwar tattalin arzikin kungiyar EU da kuma cinikayya a tsakanin kasa da kasa, kwamitin zai tantance shi daga dukkan fannoni, musamman ma tasirin da zai haifar wa kasuwar 'yan kwadago ta nahiyar Turai. Kwamitin kungiyar EU da kuma sassansa suna bukatar wasu watanni domin tattara bayanai, kuma za su ba da shawara a hukunce a karshen rabin wannan shekara.(Lami)