EU ta kaddamar da wani aikin jin ra'ayin jama'a kan matsayin tattalin arzikin kasuwa na kasar Sin
Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta kaddamar a ranar Laraba da wani aikin jin ra'ayin jama'a domin sanin ko ya dace ko a'a kan baiwa kasar Sin matsayin wata kasuwar tattalin arziki (SEM), ta hanyar neman jin ra'ayoyi domin kimantawa cikin zurfi tasirin sauya matsayin tattalin arzikin kungiyar EU. Bisa budewar da za ta kwashe tsawon makwanni goma, jin ra'ayin jama'a ta hanyar intanet ya shafi hanyoyin da aka yi amfani da su a lokacin gudanar da ayyukan "anti-dumping" na EU kan kayayyakin kasar Sin da ke shigo da su, alhali kuma cewa matakan na yanzu za su kammala a cikin watan Disamba, in ji kwamitin Turai, wata babbar hukumar zartaswa ta EU, a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku