in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar EU ta yi kashedi ga kasashe 19 da suka keta dokar ba da mafaka ga 'yan gudun hijira
2015-09-24 10:57:00 cri
Hukumar EU ta yi kashedi ga mambobin kasashen kungiyar 19 da suka keta dokoki har sau 40 yayin da suka daidaita batun 'yan gudun hijira, inda ta zargi wadannan kasashe saboda ba su iya gudanar da manufar ba da mafaka ga 'yan gudun hijira na kungiyar EU yadda ya kamata ba.

Wadannan kasashen da aka zarge su sun hada da Jamus, Faransa, Girka, Austria, da Hungary da Poland.

Kungiyar EU ta nuna cewa, ya zama dole wadannan kasashe su mayar da martani bayan da suka samu wasikun kashedi cikin watanni biyu. Idan kungiyar EU ta ci gaba da ganin wadannan kasashe ba su dauki matakai yadda ya kamata ba, kuma ba su kyautata ayyukansu ba, to za a kai su kara zuwa babbar kotun Turai.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China