Ana dai kallon wannan ziyara ta Mogherini a matsayin wani mataki da zai kara sa kaimi ga mu'amala tsakanin kasashen Turai da Cuba.
Hukumar harkokin waje ta kungiyar EU ta yi bayanin cewa, lokacin wannan ziyara da Mogherini ta kai yana da muhimmancin gaske wajen gudanar da shawarwari tsakanin EU da kasar Cuba. Kuma Mogherini za ta gana da ministan harkokin wajen kasar Cuba Bruno Rodriguez, da sauran jami'an kasar domin tattauna batutuwa game da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, da ma sauran batutuwa. (Zainab)