in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen EU da dama sun yanke shawara karbar karin 'yan gudun hijira na kasar Sham
2015-09-12 14:12:45 cri
Shugaban kwamitin kungiyar kawancen kasashen Turai EU Jean-Claude Juncker ya gabatar da shirin karbar 'yan gudun hijira na kasar Sham da EU ta tsara a ranar laraban da ya gabata 9 ga wata, inda aka samu bambancin ra'ayi tsakanin mambobinta.

Kasashe da dama na yin alkawarin karbar karin 'yan gudun hijira, gwamnatin Amurka wadda ke shan zargi daga bangarori daban-daban kan wannan batu ita kuma ta yi alkawarin karbar karin 'yan gudun hijira na kasar Sham dubu 10 saboda ganin matsin lambar da ake mata.

Ministan shari'a na kasar Ireland Madam Frances Fitzgerald ta sanar a ran 10 ga wata cewa, gwamnatin kasar ta yanke shawarar karbar karin 'yan gudun hijira 2900 bisa adadin da EU ta tanada ma kasar ta karba. Haka nan ita ma Ireland za ta karbi 'yan gudun hijira 4000 a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Ban da wannan kuma, ministan harkokin cikin gida na kasar Croatia Mista Ranko Ostojic ya bayyana a wannan rana cewa, kasar ta yarda ta karbi karin 'yan gudun hijira bisa sabon shirin da EU ta tsara, wanda ya tanadi cewa Croatia za ta karbi 'yan gudun hijira 1614 dake gudu zuwa kasashen Greece, Italiya da Hungary.

A nashi bangare kuma, kakakin fadar shugaban kasar Amurka ta White House Misa Josh Earnest ya ce, shugaban kasar Obama ya nemi gwamnati da ta bude kofar kasar ga 'yan gudun hijira dubu 10 a cikin sabon shekarar hada-hadar kudi ta 2016, amma adadin bai kai wanda wasu kungiyoyin kasa da kasa suka tanada ma Amurka ta karba ba.

An ba da labari cewa, saboda 'yan gudun hijira sun kutsa cikin wasu kasashe, sai ra'ayin kabilu na wurare daban-daban da ra'ayin nuna wariyar launin fata suka kunun kai, hakan kuma ya fi i tsanani. A daren ranar alhamis 10 ga wata, an cinna wuta kan gidajen da aka tsugunar da 'yan gudun hijira a yankin Gerstungen dake jihar Thüringen a gabashin kasar German. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China