Babban wakilin kungiyar EU mai kula da manufofin diflomasiyya da tsaro Federica Mogherini ya ba da wata sanarwa a wannan rana, inda ya nuna cewa, kotun ta yanke hukunci kan wannan batu ne kamar yadda aka tsara, bai yi karin bayani kan ko ya dace a fitar da kungiyar ta Hamas daga jerin kungiyoyin 'yan ta'adda ba.
Ya kara da cewa, yaki da ta'addanci ya kasance wani muhimmin aiki da kungiyar EU ta sanya a gaba, sannan tana da niyyar toshe dukkan hanyoyin da kungiyoyin 'yan ta'adda ke samun kudadensu. Kana, hukumomin kungiyar EU da abin ya shafa za su ci gaba da dukufa kan wannan aiki bisa fannoni daban daban, domin fuskantar dukkan kalubalen da za su iya kunno kai idan aka cire kungiyar Hamas daga jerin kungiyoyin ta'addanci a nan gaba.
Bugu da kari, cikin sanarwar, Federica Mogherini ya kuma bayyana cewa, za a dakatar da hukuncin da kotun ta yanke bayan kwamitin Turai ya daukaka kara kan batun, sa'an nan, kotun tarayyar Turai, watau hukumar shari'a ta koli ta kungiyar EU za ta yanke hukunci na karshe kan wannan lamari. (Maryam)