Mr Tsipras ya ce, a matsayin hukumar demukuradiyya ta kungiyar EU, ya kamata majalisun dokokin kasashen Turai su taka muhimmiyar rawa, inda ya jaddada cewa, Girka ta zama wata kasa ce ta farko da aka yi gwajin gudanar da manufar tsuke bakin aljihu, abun da ya zama ba'a yi nasara ba. Dalilin da ya sa Firaministan ya ce ya kamata a yi la'akari da halin da ake ciki. An ba da labarin cewa, hakan ya zama rikicin Girka, amma a zahiri dai, ya kasance rikicin kasashen Turai ne baki daya, saboda kasashen Turai ba su iya samu wata hanyar warware matsala ba. Girka dai tana fatan samun shirin tallafi don biya bashi, ba ci gaba da bin bashi ba.
A ranar 8 ga wata, fadar shugaban kasar Faransa ta ba da wata sanarwa, inda ta ce, a wannan rana, shugaban kasar François Hollande ya ce, burin kasashen da ke amfani da kudin Euro shi ne, a bar Girka ta zama wata mambar dake cikin kungiyar, kuma idan aka so cimma burin, dole ne Girka ta ba da shawarwari yadda ya kamata.(Bako)