in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kungiyar EU sun bukaci da a daddale yarjejeniyar tallafawa Girka
2015-07-08 13:32:07 cri

An kammala taron koli na kasashen da suke amfani da kudin Euro a daren jiya Talata 7 ga wata, inda a gun taron manema labaru da aka shirya bayan taron, aka bayyana bukatar tsara wani shiri na tallafawa Girka game da masu bin kasar bashi, wanda zai kunshi matakan gyare-gyare daga dukkanin fannoni.

A yayin taron na manema labarun da ya gudana, shugaban kwamitin kungiyar EU Jean-Claude Juncker, ya ce idan aka gaza daddale yarjejeniya, kamfanonin kasar Girka na iya durkushewa, kuma tsarin bankunan kasar shi ma zai rugurguje. Kaza lika jama'ar kasar za su fada cikin wahalhalu, matakin da kuma zai haifar da mummunan tasiri ga nahiyar Turai baki daya.

Har wa yau dai a taron, Juncker ya ce yana matukar adawa ga matakin Girka na janyewa daga tarayyar kasashen da ke amfani da kudin Euro. Amma idan Girkan ba ta dauki matakin da ya wajaba ba, akwai yiwuwar janyewar jikin kasar daga tarayyar.

A daya hannun kungiyar EU ta shirya sosai game da shirin janyewar Girkan daga kungiyar kasashen da ke amfani da kudin na Euro, a sa'i daya kuma ta tsara shirin tallafi gare ta.

A ranar 12 ga watan nan ne ake fatan sake gudanar da wani taron kolin kungiyar ta EU, domin tattauna shirin warware rikicin bashin na Girka, da kuma tsara wa'adin karshe na tallafawa kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China