Shugabannin kungiyar EU sun yi taro kan matakan magance matsalar 'yan gudun hijira
Shugabannin kasashen mambobin kungiyar tarayyar Turai (EU) sun gudanar da wani taron da ba na hukuma ba a birnin Bruxelles a ranar Laraba da yamma, domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar 'yan gudun hijira da kuma wajibcin bullo da tsarin da ya dace na kula da matsalar a siyasance. Taron da shugaban kwamitin tarayyar Turai, Donald Tusk ya bukaci a gudanar, an shirya shi a ranar ta Laraba da yamma.
"Mun dauki wasu karin matakai a tun daga yau. Wannan shi ne abin da kasashen Turai suka fi bukata, wannan wata hanya ce ta samun zarafin warware matsalar 'yan gudun hijira", in ji faraministan Burtaniya David Cameron a yayin zuwansa a taron, tare da jaddada cewa dole ne a tabbatar da zaman lafiya a cikin wadannan kasashe da yankunan da 'yan gudun hijira suke fitowa. (Maman Ada)