Sanarwar ta ce, tare da tsanantar batun 'yan gudun hijira a yankin tekun Bahar Rum da iyakar kasashen kungiyar, hukumar kungiyar EU ta dauki niyyar kara kulawa da baki, ta hanyar ceton rayukansu, da yin hadin gwiwa da kasashe abokai, da yaki da fataucin mutane, da kuma tsara tsarin kulawa da 'yan gudun hijira da iyakar kasa cikin dogon lokaci da sauransu.
A ranar Alhamis ne dai, hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ta ba da wani rahoto dangane da yanayin da ake ciki na yin gudun hijira a duk fadin duniya a shekarar 2014 a Geneva, inda aka bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, yawan baki 'yan gudun hijira ya kai miliyan 59.5 a duniya, wanda ya karu da miliyan 8.3 bisa na shekarar 2013, yayin da yawansu ya kusan rubanyawa bisa na shekarar 2004. Saurin karuwar yawan 'yan gudun hijira a bara ya fi duk sauran shekarun baya.(Fatima)