Sanarwar ta bayyana cewa, ba za a amince da matakan da Rasha ke dauka ba na kokarin mallakar yankin Crimea ba bisa doka ba, lamarin da a cewar sanarwar ya haddasa rashin zaman lafiya a yankin gabashin kasar Ukraine, don haka a cewar wannan sanarwa tilas ne Rasha ta dakatar da abin da take yi a wannan yanki.
Har ila yau sanarwar ta yi kira ga kasar Rasha, da ta amince da sakamakon zaben kasar Ukraine, ta kuma janye sojojinta daga iyakar kasar Ukraine, ta hana shigar da makamai ko dakaru shiga kasar Ukraine, sa'an nan ta kuma matsawa dakaru masu adawa da hukumomin kasar Ukraine wajen ganin sun ajiye makamai su kuma dakatar da tada zaune tsaye.
A karshen watan Maris din da ya gabata, da kuma karshen watan Afrilu, kasar Amurka da kungiyar EU, sun sakawa kasar Rasha takunkumi sau biyu, bisa dalilin su na nuna rashin amincewa da tsoma bakin da Rasha ke yi cikin harkokin gidan kasar Ukraine. (Zainab)