Manzon na MDD ya jaddada cewa, takardun gayyata na shawarwarin za a aike da su a ranar Talata, kuma shawarwarin za su kwashe tsawon watanni shida.
Mista De Mistura ya shaidawa 'yan jarida cewa, mulki na gari, sabon kundi da sabbin zabubbuka za su kasance a kan tebur a ranar shawarwarin wanda makasudinsu shi ne na cimma wani tsagaita wuta mafi fadada, yaki da barazanar kungiyar IS da kuma bunkasa taimakon jin kai a kasar Syria.
Wannan lokaci ne na yin kokari domin tattara sakamako mai kyau, in ji mista De Mistura, tare da kara nuna cewa shawarwarin ba za su sake maimaita abin da ya faru a yayin shawarwarin da suka gabata ba.
Duk kokarin gamayyar kasa da kasa wanda ya kai ga shirya wani taron kasa da kasa kan Syria wato Geneva II a farkon shekarar 2014, shirin warware rikicin Syria na cikin karo da kalubale har kullum, dalilin babban sabanin dake gwamnati da masu adawa, da kuma yawan kungiyoyin 'yan ta'adda masu kaifin kishin Islam dake cikin kasar, lamarin dake kara tsananta rikicin na Syria. (Maman Ada)