Wannan ya sa a jiya Alhamis manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria Staffan Demistura ya ce, kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa na kasar Syria su yi amfani da wannan kyakkyawar damar neman sulhu yadda ya kamata.
A sa'i daya kuma, ana ci gaba da yake-yake a kasar Syria, inda a kwanakin baya sojojin gwamnatin suka samu nasarori da dama a fafatawar da suke yi.
A jiya ne kuma shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya gana da takwaransa na kasar Iran Hassan Rouhani a babban birnin kasar, Paris. Bayan ganawar tasu ce, shugaba Hollande ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, ya kamata a gaggauta samarwa kasar Syria taimakon jin kai, da kuma yi shawarwari a kokarin da ake na gudanar da zabe a kasar.
A nasa bangare, shugaba Rouhani ya ce, ya kamata jama'ar Syria su tsara makomarsu da kansu, haka kuma, a halin yanzu, manyan kalubalolin da kasar ke fuskanta su ne ta'addanci da kuma kungiyar masu tsattsauran ra'ayi na IS.
Rahotanni daga kasar Faransa na cewa, mai yiyuwa ne kasar Syria ta sake jinkirta taron shawarwarin neman sulhu, sabo da jam'iyyar adawa ta kasar ba ta yanke shawara kan ko za ta halarci taron ko a'a ba. (Maryam)