Su dai manyan kungiyoyin adawar kasar sun zargi gwamnatin Syriar da kuma sojojin kasar Rasha da yin kafar ungulu a yunkurin tattaunawar zaman lafiyar kasar.
An shirya tattaunawa tsakanin jakadan MDD na musamman a kan batun Syria Staffan de Mistura tattaunawa da manyan kungiyoyin adawar Syria a karo na biyu da marecen ranar Talatar nan a helkwatar ofishin MDD, amma daga bisani aka soke taron tattaunawar.
Sanarwar wacce aka rabawa manema labaru da yammacin ranar Talata, ta ce babu wata sauran tattaunawa tsakanin bangarorin Syriar.
A maimakon gudanar da taron tattaunawar a ofishin MDD dake birnin Geneva, jami'an 'yan adawar Syria sun kira taron manema labarai, inda suka bayyana cewar, an samu sabon rahoton barkewar tashin hankali inda dakarun Rasha da mayakan gwamnatin Syria a daren da ya gabata sun zafafa kaddamar da hare hare a biranen Homs da Aleppo, da suka hada da kaddamar da hare haren kan asibitoci da muhimman gine gine. Harin wanda aka yi yunkurin afkawa fareren hula. (Ahmad)