"Ba karshe ne ba, ko kuma wani rashin nasara a shawarwarin" in ji mista De Mistura, tare da jaddada wajibcin kara 'yin aiki a wannan fanni.
Haka kuma, ya bayyana fatan ganin an shirya wani taro cikin gaggawa idan dama ta samu na gungun kasa da kasa da ke taimakawa Syria, dake kunshe da kasashen Amurka, Rasha, Iran da Saudiyya da aka tsaida shirya da farko a ranar 11 ga watan Febrairu a birnin Munich na kasar Jamus. (Maman Ada)