in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin kasar Syria sun samu ci gaba a yakin kasar a arewacin kasar
2016-01-25 10:05:08 cri
A jiya ne sojojin gwamnatin kasar Syria suka samu ci gaba a fafatawar da suke yi a jihar Lattakia ta arewacin kasar inda suka yi nasarar kwato garin Rabia, muhimmin sansanin dakaru masu adawa na kasar.

Wani jami'in bangaren soja na kasar Syria ya bayyana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kwato garin Rabia dake da nisan kilomita 60 daga arewa maso gabashin birnin Lattakia ne sakamakon taimakon sojojin fararen hula da ke wurin. Shi dai wannan wuri yana dab da kan iyakar Syria da Turkiya ne. Sojojin injiniyoyi na gwamnatin kasar suna gudanar da aikin kawar da boma-boman da dakarun masu adawa suka binne a garin.

Rahotanni daga kasar Syria na cewa, garin Rabia yana daya daga cikin manyan sansanonin dakarun masu adawa dake jihar Lattakia. A 'yan makwannin da suka gabata, sojojin gwamnatin kasar Syria sun samu babban ci gaba a yankin arewacin jihar Lattakia, inda suka kwato garuruwa da dama. Bayanai na cewa, sojojin gwamnatin kasar za su ci gaba da dannawa zuwa kan iyakar kasar da ke gabashin jihar Lattakia da jihar Idlib. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China