Dangane hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasa ta Sin Lu Kang ya bayyana a yau Litinin cewa, yin shawarwarin neman sulhu ita ce hanya kacal da za a iya warware batun Syria da kuma samun sakamako mai gamsarwa.
Kaza lika, ya ce, ya kamata bangarorin biyu da rikicin kasar ya shafa su karfafa fahimtar juna a tsakaninsu, ta yadda za a cimma nasarar shawarwarin, sa'an nan kuma, ya kamata gamayyar kasa da kasa, musamman ma kasashen dake yankin su taimaka yadda ya kamata. Kasar Sin ita ma za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa domin ciyar da aikin warware matsalar Syria ta hanyar siyasa gaba. (Maryam)