in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya soki bama baman da aka jefa a Damascus,tare da bukatar samun cigaba a tattaunawar Geneva
2016-02-02 10:54:13 cri
Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya soki munanan hare-haren bama bamai da aka kai har sau uku a kusa da wani dakin ibada a kudancin birnin Damascus, yana mai kira da a gaggauta samun cigaba a tattaunawar zaman lafiya na Geneva da yanzu haka ake yi.

Mr Ban ya soki mummunan harin da ya auku kusa da wajen ibadar Sayyidah Zayban a ranar lahadi inda mutane fiye da 60 suka halaka.

A cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar babban magatakardan MDD Yace ya kamata a kama duk wadanda ke da alhakin wannan harin akan fararen hula tare da lura cewar masu tsatsauran ra'ayin na kungiyar IS sun rigaya sun sanar da kai wannan harin.

Mummunan harin ya zo daidai da bude taron tattaunawar zaman lafiiya na Geneva.

Ya jaddada cewar al'ummar kasar Syria suna bukatar ganin sakamako zahiri a Geneva. A cewar shi yana da muhimmanci cewar gwamnati da 'yan adawan na Syriya su amince akan samun cigaba cikin gaggawa game da yanayin jin kai, warware rikin siyasa da zai biya bukatun al'ummar kasa da kuma dakatar da bude wuta.

Mr Ban ya kuma yi kira ga duk jam'iyyun kasar da ma kasashen duniya da su yi amfani da wannan dama ta ingiza ganin cigaba da samar da yanayin jin kai, sakin wadanda aka tsare da kuma dakatar da bude wuta nan take.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China