De Mistura ya shaida ma manema labarai bayan ganawa da 'yan adawan a yammacin wannan rana cewar batun jin kai da 'yan adawan suka kawo a lokacin ganawar shi ma wani murya ne na jama'ar kasar kuma dole a saurari muryar a lokacin tattaunawar.
Yace ba kawai za'a yi tattaunawa a Geneva bane har ma za'a samar da wani abu da al'ummar Syrian zasu gani su kuma taba. Yana mai bayanin cewa rikicin kasar Syrian ya riga dade har shekaru shida a cikin shekara na 6 al'ummar kasar ne sun wahala kwarai don haka dole a samu wani sabon abu a cikin tattaunawar.
Yace zai gana da wakilan gwamnatin kasar Syrian a talatan nan sannan tawagar zasu yi tattaunawa mai zurfi akan batutuwan da yafi jawo hankalin kowa a baya bayan nan musamman muhimmin batu na dakatar da bude wuta.