Riad Hibjab, shi ne jami'in tsare-tsare dake wakiltar kungiyoyin 'yan adawa, ya shedawa 'yan jaridu tun a daren Laraba cewar, ba za a samu zaman lafiya ba, idan har Bashar al Assad ke ci gaba da mulki kuma sojojin waje ke tsoma bakinsu cikin harkokin kasar ta Syria.
Hibjab, ya zargi gwamnatin Syria cewar ba da gaske take ba kan shirin zaman lafiya a rikicin da ya dabaibaye kasar, yana mai cewa, 'yan adawar kasar suna sane da cewar gwamnatin Syriar ce ta yi kafar ungulu a yunkurin tattaunawar sulhun da aka shirya gudanarwa a Geneva.
Ya kara da cewar, tawagar jami'an dake wakiltar gwamnatin Syriar sune suka kawo cikas wajen samun nasarar tattaunawar da aka kaddamar a makon jiya.
Sai dai wani tsokaci da wakilin MDD na musamman kan rikicin Syria Staffan de Mistura ya gabatar, ya ayyana ranar 25 ga wannan wata na Fabrairu a matsayin ranar da za'a dawo bude tattaunawar.
Mistura, ya shedawa 'yan jaridu cewar, jinkirin da aka samu ba ya nuna cewar tattaunawar ta wargaje ba ne, a cewar sa dukkanin bangarorin na da jan aiki a gaban su. (Ahmad)