A wannan rana, babban kwamitin jam'iyyun adawa da gwamnatin Syria da ke kula da yin shawarwari (HNC) dake birnin Riyadh, hedkwatar Saudiya ya ce, kwamitin HNC zai tura wata tawaga zuwa Geneva a yau Asabar 30 ga wata, domin halartar shawarwarin.
A jiya, kakakin kwamitin HNC ya bayyana cewa, bayan sakataren harkokin waje na Amurka, John Kerry ya yi alkawarin biyan bukatun jam'iyyun adawa , kwamitin ya dauki niyyar shiga shawarwarin. A don haka, za su kai ziyara a Geneva domin yin shawarwari da gwamnatin Syria kan ba da taimakon jin kai ga garuruwan kasar da aka kange cikin dogon lokaci. Idan gwamnatin Syria ta mai da hankali kan shawarwarin, za a ci gaba da wannan shawarwari. In ba haka ba, za su janye jiki daga shawarwarin.
An ba da labarin cewa, za a yi shawarwari kan batutuwa da yawa a wannan karo, kamar su tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci, da amincewa da yin jigilar kayayyakin jin kai zuwa kasar, da yaki da ta'addanci, da gyara kundin tsarin mulkin kasa, da gudanar da babban zabe da dai sauransu. (Fatima)