in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 53 sun mutu sakamakon hadarin mota a kasar Ghana
2016-02-18 19:42:47 cri

Rundunar 'yan sandan kasar Ghana ta bayyana cewa, mutane 53 sun mutu kana a kalla 23 suka jikkata, bayan da wata motar safa da ta taso daga birnin Kumasi a kan hanyarta ta zuwa Tamale dake arewacin kasar, ta yi karo da wata motar daukar kayayyaki jiya da dare kimanin kilomita 420 daga birnin Accra.

Bayanai na cewa, wannan shi ne hadari mafi muni da aka tafka a 'yan shekarun nan, yanzu 'yan sanda na kokarin gudanar da bincike don gano musabbabin hadarin

Ban da wannan kuma, bayan aukuwar lamarin, shugaban kasar Ghana John Mahama ya mika ta'azziya ga dangogin wadanda suka mutu a shafin sada zumunta naTwitter. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China