An kaddamar da aikin gina sabuwar tsangayar jami'ar nazarin kiwon lafiya da kimiyya ta kasar Ghana ranar Alhamis din nan, wanda wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyi.
An gina wannan sabuwar tsangaya ne a garin Ho domin makarantar nazarin kwayoyin halittu da magunguna ta jami'ar, wadda ke da tazarar kilomita 138 daga Accra, babbban birnin kasar.
Kamfanin kasar Sin mai suna Yanjian Group na hadin gwiwa da gwamnatin kasar Sin ne ya gudanar da aikin, a matsayin wani bangare na bada tallafi ga gwamnatin kasar Ghana, sannan kimanin dalar Amurka miliyan 17 ne kamfanin ya kashe, yayin da ita ma gwamnatin Ghana ta bada nata kason na dala dubu 940.
Gine-ginen sun hada da samar da filin wasanni da wuraren aje ababen hawa da gina hanyoyi da kuma da sauran muhimman kayayyaki.
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya halarci bikin kaddamar da aikin, kuma ya nuna gamsuwarsa da irin gudumowar da kasar Sin ke baiwa kasarsa, sannan ya bayyana irin wannan taimako a matasayin wani al'amarin da zai kara dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.
Jakadar kasar Sin a Ghana Sun Baohong, ta bayyana cewar kamar yadda Ghana ta bukaci a samar da kujerun zama da sauran muhimman kayayyaki a jami'ar, kasar Sin ta yi na'am da wannan bukata.
Jami'ar ta Ghana, wacce ta fara aiki a shekarar ta 2012 da dalibai kimanin 155, a halin yanzu, jami'ar na da dalibai 2,044. Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta hakikance cewar jami'ar ce a kan gaba cikin cibiyoyin da ake gwajin alluran rigakafin cutar Ebola a duniya.(Ahmad Fagam)