in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta inganta kokarinta na shawo kan cutar sankarau ganin mutane 32 sun mutu
2016-01-26 10:46:04 cri

Kasar Ghana ta inganta wayar da kan al'ummarta da kuma sa ido a unguwanni da suka samu bullar cutar sankarau, kamar yadda wani jami'in kiwon lafiya ya tabbatar a ranar Litinin din nan.

Wannan mataki dai an dauke shi ne da nufin dakile bazuwar cutar da yanzu haka adadin wadanda suka mutu sakamakonta ke karuwa a wassu sassan kasar.

Mataimakin ministan kiwon lafiyar kasar Victor Bampoe ya ce, gwamnati ta ware kudi cedis 150,000 domin yaki da wannan cuta, wadda yanzu haka ta riga ta hallaka mutane 32 ta kuma kama guda 150.

Ya ce yana fatan adadin kudin da kuma horas da jami'an kiwon lafiya a ko ina dake fadin kasar zai taimaka wajen kara dakile bazuwar cutar, sannan ya ce ma'aikatarsa ta dauki matakai na tabbatar da cewar, cutar ba ta fi karfin kasar ba.

Har ila yau ya yi kira ga marasa lafiya da su je asibiti da wuri don a duba su.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China