in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum guda ya rasa ransa, wasu da dama sun jikkata a sanadiyyar fashewar wani abu a wurin fasa dutsen kasar Ghana
2015-12-25 10:01:27 cri
Kafafen yada labarai na kasar Ghana, sun rawaito cewar a ranar Larabar da ta gabata ne wani mutum guda ya gamu da ajalinsa, sannan wasu da dama suka jikkata a sakamakon fashewar wasu abubuwa a wani wurin fasa dutse dake da tazarar kilomita 40 daga Accra babban birnin kasar Ghana.

A cewar Nketia Yeboah, Daraktan hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda shiyya a gabashin kasar ya ce, fashewar dai ta afku ne a wani wurin fasa duwatsu na kamfani na Akuabo wanda aka yi watsi da shi sama da shekaru 4 da suka gabata.

Yeboah, ya kara da cewar, ana cigaba da duba lafiyar wadanda suka samu raunuka a wani asibitin gwamnati na Nsawam, yayin da wasu daga cikinsu sun riga suka koma gida bayan da aka yi musu jinya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China