Haka kuma, a cewar wani jami'in sashen binciken cututtuka na ma'aikatar lafiyar kasar, an fara ganin alamar barkewar cutar sankarau a birnin Brong Ahafo daga karshen watan Disamba da ya gabata, ya zuwa yanzu, mutane sama da 160 ne a larduna biyar suka kamu da cutar, yayin da mutane 38 suka rasu sakamakon kamuwa da cutar .
Bugu da kari, ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce, hukumomin da abin ya shafa sun dukufa yadda ya kamata domin kawo karshen yaduwar cutar a kasar. (Maryam)