in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana da Italy zasu tallafa wajen warware rikice rikice da matsalar 'yan gudun hijira a kasashen duniya
2016-02-04 11:19:49 cri
Kasashen Ghana da Italy sun kuduri aniyar tallafawa kasahen dake fama da rikici kamar Libya da sauran kasahe masu tasowa, a wani mataki na rage kwararar bakin haure zuwa kasashen turai a sanadiyyar tashe tashen hankula a 'yan shekarun nan.

Kasashen biyu sun yi amanna cewar idan har aka samar da guraben aiki masu yawa ga matasa a kasashen, hakan zai rage musu sha'awar yin kaura zuwa Turai domin neman ayyuka masu tsoka.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da kasar Ghana zata ci gaba da aiwatarwa shine, zata karawa kasar Italy kwarin gwiwa data hada kai da kungiyar tarayyar turai kuma ta jajurce wajen tallafawa kasashen dake fama da rikici irinsu Libya wajen kafa gwamnatoci da zasu zauna da gindin su.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama shi ne ya sanar da hakan a lokacin shirya wata liyafar cin abinci don karrama Firaiministan Italy Matteo Renzi, wanda yaje ziyarar aiki kasar.

Mahama, ya jaddada bukatar kasashe masu arziki dasu tallafawa kasashe masu tasowa da masu fama da rikice rikice, ta hanyar kakkafa masana'antu domin samarwa matasa ayyukan yi, a ganinsa hakan zai rage yawan cincirundon da mutane ke yi zuwa kasashen yammacin Turai. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China