in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na fatan samar da ruwan sha ga al'ummar ta nan da shekara ta 2025
2015-11-25 11:17:29 cri

Ghana tana fatan cimma samar da wadataccen ruwan sha ga daukacin al'ummar kasar ta nan da shekara ta 2025, kamar yadda ministan ruwa, ayyuka da gidajen kasar Kwaku Agyemang-Mensah ya sanar a ranar Talatar nan.

Mr. Agyemang-Mensah ya sanar ma manema labarai a Accra babban birnin kasar cewa, Ghana ta samu bashin kudi har dalar Amurka miliyan 48 daga bankin duniya domin magance kalubalen da ake fuskanta na rashin wadataccen ruwan sha a birnin.

Ya ce aikin zai taimaka wajen shawo kan matsalolin dake tattare da rashin ruwa, ya kuma inganta samar da ruwa a ko ina. A yanzu haka ya yi bayanin cewa, kasar ta riga cimma wani matsayi na samar da ruwan sha mai tsabta ga al'ummar kasar na tsawon shekaru.

Ministan ya ce, Gwamnatin kasar Sin yanzu haka ta rattaba hannu tare da kasar ta Ghana domin samar da rijiyar burtsatsi guda 1,000 ma mazauna yankunan mulki guda 10.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China