Wani jami'in ma'aikatar cinikayya da masana'antu ta kasar ya ce, ana fatan kasar Sin za ta kara zuba jari a kasar Ghana.
Haka kuma, jakadan kasar Sin dake kasar Ghana madam Sun Baohong ta bayyana cewa, an shirya dandalin a lokacin cikon shekaru 55 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin Sin da Ghana domin kafa wani dandali ga kamfanonin kasashen biyu wajen yin sharwari da kuma samar da karin damar yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Gwamnatin kasar Sin na sa kaimi ga kamfanonin kasashen Sin da Afirka wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin samar da kayayyakin more rayuwa da kuma habaka masana'antu, kuma tana fatan kamfanonin kasashen biyu za su iya kara samun ra'ayi daya a fannonin da abin ya shafa, ta yadda za a iya kyautata hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya zuwa wani sabon matsayi.
Kuma ana imani cewa, hanyar cimma moriyar juna ita ce hanyar samun ci gaba na dindindin.
Bisa kididdigar da cibiyar raya harkokin zuba jari ta kasar Ghana ta samar, an ce, adadin kayayyakin da kasar Ghana ta fitar zuwa kasar Sin ya kai dallar Amurka biliyan 1.4 a shekarar 2014, wanda ya kasance wani babban ci gaba a wannan fannin. (Maryam)