in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana zai kai ziyara Iran
2016-02-14 11:48:13 cri
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, zai fara ziyarar aiki a kasar Iran tun daga ranar Lahadin nan, kamar yadda wata sanarwa ta fadar shugaban kasar ta bayyana.

Ana sa ran yayin ziyarar, shugaba Mahama da mai masaukin sa Hassan Rouhani, za su tattauna game da al'amuran da suka shafi kasashen su.

Mahama, zai zama shugaba na baya bayan nan da zai ziyarci kasar Iran, tun bayan dage wa kasar takunkumi, zai kuma halarci taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaba Rouhani a Lahadin nan. Har wa yau za a shirya masa liyafar ban girma, baya ga halartar sanya hannu da zai yi kan wasu takardun fahimtar juna tsakanin kasashen biyu.

Kaza lika shugaban na Ghana zai gana da shugaban addinin kasar Ayatollah Khamenei, sa'an nan zai tattauna da shugaban majalissar dokokin kasar Ali Larijani.

Ghana da kasar Iran dai na da dadadden kawance na shekaru masu yawa. A kuma shekarar 2014, yayin ziyarar da shugaban na Ghana ya kai kasar, ya tattauna da tsohon shugaban ta Mahmoud Ahmadinejad, a kuma wannan karo ne kasashen biyu suka kafa wata hukumar hadin giwa ta samar da ci gaba, da cimma moriyar juna tsakanin su.

Ghana na fatan yin hadin gwiwa da Iran a fannin bunkasa ayyukan gona, da hakar ma'adanai, ta yadda hakan zai ba ta damar fitar da kayayyaki ta zuwa Iran, baya ga kudurorin bunkasa sha'anin kasuwanci tsakanin sassan biyu, wanda shugaba Mahama zai gabatar, a yayin taron 'yan kasuwa da zai gudana lokacin ziyarar ta sa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China