Wannan runduna, ita ce za ta jagoranci duk wasu ayyuka na liken asiri dangane da zaben, da kuma samar da duk wasu muhimman bayanai ga sauran jami'an tsaron kasar game da sha'anin zaben.
Woyongo, ya bukaci dukkannin hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a kasar, da su tsara dukkannin dabarun da za su taimaka waje samun nasarar zabukan kasar cikin lumana, kamar yadda suka saba aiwatarwa a shekarun baya.
Tawagar dai ta kunshi wakilai daga dukkanin bangarori da hukumomin tsaro na shiyyoyi da majalisar koli ta kasar.
Mai rikon mukamin babban sifeton 'yan sandan kasar John Kudalor, ya ce, batun zabe al'amari ne mai muhimmanci, wanda ya fi karfi a danganta shi da duk wani soki burutsu ko da ta husuma, wanda ka iya haifar da barazanar tsaro ga kasar, ya kara da cewar za su dauki dukkanin matakan da suka dace kan duk wasu kungiyoyi ko jamiyyun siyasa masu daukar doka a hannun su. (Ahmad)