in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ta ce shirinta a kan Ghana yana kan hanya
2016-02-06 12:41:14 cri
Asusun bada lamuni ta duniya IMF ta ce shirin da ta yi na aiwatar da ayyukan ba da taimako na tsawon shekaru 3 a Ghana yana kan hanya.

Mataimakin babban darakata Zhu Min ya sanar da hakan a taron manema labarai da aka yi a birnin Accra lokacin taron hada kididdaga da asusun ta shirya ma nahiyar Afrika.

Ya ce bayan sake nazari karo na biyu wanda aka kammala kusan makonni biyu da suka shude, an lura da cewa, Ghana tana kan hanya dangane da shirinta tare da asusun. A saboda hakan ake maraba da cikakken himmar da gwamnati ta nuna da kuma aniyarta na kula da basussuka da rage karuwan gibin kudin.

Mr Zhu ya lura da cewar manajojin tattalin arziki suna iyakacin kokarin samun ci gaba wajen rage yawan basuka.

Ya bayyana cewa asusun tana ganin yadda karancin gibin da ake samu ya kara yin kasa daga kashi 10% zuwa kashi 7% har ma ya kara komawa kashi 5% wand ba karamin ci gaba ba ne.

Basusukan kuma shi ne a kan gaba cikin matsalolin don haka dole a samu yin tattali da samar da hanyoyin shawo kansu wanda su ne a kan gaba.

Mataimakin babban daraktan ya ce idan aka samu nasarar sauko da yawan basusukan za'a samu sauran alkalumma su sauko. Dole ne a yi hakan a yanzu ta yadda masana'antu masu zaman kansu za su iya ammfana a shekara mai zuwa. Zhu Min sai dai ya yi kira da a kara daukan mata kai daga bangaren gwamnati kuma ana bukatar a tabbatar da ana da rarar kusan kashi 2% a wannan shekarar ta yadda za'a iya tafiyar da raguwar bashin, idan aka yi hakan to ana bukata wani mataimaki da zai sassauta wannan bangaren.

A cewar shi abin da Ghana take bukatar ta yi, shi ne yin kwaskwarima a bangaren kudinta, inganta tare da karfafa sashin harajinta, sannan ta magance aukuwar kaucema biyan haraji ta kuma inganta mataikin kashe kudade na jama'a. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China