in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauyin yanayi ya haddasa kamfar ruwa a kasar Ghana
2016-02-18 10:47:55 cri

Wasu yankuna a kasar Ghana na fama da matsalar karancin ruwan sha kasancewar famfunan dake bayar da ruwan sun tsaya cik, sannan ainihin tashoshin dake samar da ruwan sun kafe.

Dunbum matsaloli da suka hada da mummunan fari, da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba na daga cikin dalilan da suka haddasa wannan ibtila'i a kasar, wacce ta sha alwashin samar da wadataccen ruwan sha a kasar zuwa shekarar 2025.

Wani mazaunin yankin Nsawam Adoagyiri, dake da tazarar kilomita 50 a shiyyar arewa maso yammacin babban birnin kasar, ya bayyana cewar suna cikin matsanancin kamfar ruwan sha, kasancewar tafkin Densu wanda shi ne al'ummar yankin suka dogara don samun ruwan sha daga gare shi ya kafe.

Ayyukan noma na mazauna gabar tafkin, da kona dazuka na daga cikin matsalolin da suka haddasa matsalar karancin ruwa a yankunan kasar ta Ghana.

Ba wani sabon abu ba ne ka ga yara kanana da mata suna dauke da kwanuka domin neman ruwan da za'a yi amfanin gida na yau da kullum.

Da ma dai, an fara fuskantar matsalar fari ne a kasar ta Ghana, tun a watan Nuwambar shekarar da ta gabata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China