An aiwatar da yarjejeniyar makaman nukiliyar kasar Iran daga ran 16 ga wata, saboda ganin haka, wasu kasashe sun sanar da kawar da takunkumin da suka garkamawa kasasr Iran ta fuskar tattalin arziki a kwanakin nan.
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Island ta ba da sanarwa a jiya Alhamis 21 ga wata don cire takunkumin iri na tattalin arziki da hada-hadar kudi da ta garkamawa kasar Iran, a yau Jumma'a 22 ga wata kuma, ministan harkokin waje na kasar Japan, Kisida Fumio ya kuma sanar da kawar da takunkumin da Japan ta garkamawa kasar Iran, tare kuma da yin shirin daddale yarjejeniyar zuba jari tsakaninta da kasar Iran a kwanakin nan baya.
Haka kuma, hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta ba da wani rahoto a ran 16 ga wata, inda ta tabbatar da cewa, Iran ta gudanar da aikin share fagen da ya wajaba don aiwatar da yarjejeniyar makaman nukiliyar kasar Iran, hakan ya sa , EU da Amurka sun sanar da cire takunkumin da suka garkamawa Iran ta fuskar tattalin arziki da hada-hadar kudi. (Amina)