Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya zargi mahukuntan kasar Iran, da yunkurin lullube ta'asar da suka tafka, ta hanyar katse alaka da kasar ta Iran. Hakan dai na zuwa ne a gabar da Iran din ke ci gaba da sukar Saudiyya, bisa hallaka wani malami mai bin akidar Shi'a tare da wasu magoya bayansa.
Rouhani wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da ministan wajen kasar Denmark Kristian Jensen, ya kara da cewa, ko kadan bai dace Saudiyya ta hallaka Al-Nimr Bakir don kawai ya soki manufofin ta ba. Sai dai duk da hakan shugaban na Iran ya ce, kasarsa za ta ci gaba da daukar matakan kyautata alakar ta da makwaftanta, ciki hadda kasar ta Saudiyya.
Ya ce matakan siyasa ne suka fi dacewa a dauka wajen magance wannan sabani da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu. Daga nan sai ya ja hankalin kasashen yankin da su hada kai da juna, don tunkari kalubalen ta'addanci dake addabar su.(Saminu Alhassan)