A gun taron manema labaru da aka shirya a Riyadh, mista Adel al-Jubeir ya furta cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta tsananta dalilin kasar Iran, a maimakon Saudiyya ko sauran kasashen Larabawa dake yankin tekun Pasha ba. Idan Iran ta ci gaba da bin manufarta a yanzu, Saudiya za ta dauki karin matakai domin mai da martani.
Kwamitin hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa a yankin tekun Pasha (GCC) ya kira taron ministoci cikin gaggawa a jiya a birnin Riyadh, inda aka yi shawarwari kan tsanantar dangantaka tsakaninsu da Iran da sauransu. Mahalarta taron suna goyon bayan matsayin da membobin kungiyar GCC suke dauka kan kasar Iran, tare da yin Allah wadai da masu zanga zangar Iran da suka kai hari kan ofishin jakadancin Saudiya a kasar.(Fatima)