in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta saki wasu sojojin ruwan kasar Amurka da ta tsare
2016-01-13 20:53:34 cri
Rundunar sojojin kasar Iran ta saki wasu dakarun sojin ruwan kasar Amurka su 10, bayan da ta tsare su tsahon kwana guda a yankin tekun Fasha.

Wata sanarwa da rundunar sojin kasar Iran din ta fitar, ta ce sojojin na Amurka na cikin wasu jiragen ruwa ne guda biyu, sun kuma kunshi maza 9 da mace daya. Sanarwar ta kara da cewa wadannan sojojin sun yiwa iyakar ruwan Iran din kutse ne, da misalin karfe hudu da rabi na yammacin ranar Talata bisa agogon wurin.

Kamfanin dillancin labarai na Press TV ya rawaito cewa sojojin na Amurka, sun yi alkawarin kaucewa sake kutse cikin iyakar ruwan Iran a na gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China