Kasar Bahrain a Talatar nan ta sanar da dakatar da zirga-zirgan jiragen sama a tsakanin ta da kasar Iran, kwana baya bayan da kasar ta goyi bayan kasar Saudiya a yanke huldar jakadanci a tsakaninsu.
Tun da farko a ranar Lahadi, kasar Saudiya ta sanar da dakatar da huldar jakadanci tsakanin ta da Iran bayan da masu zanga zanga suka afka ma ofishin ta dake Tehran sakamakon kaddamar da hukuncin kisa da ta yi a kan wani babban Malamin Shi'a Sheik Nimr Baqir al-Nimr.
A ranar Litinin kasashe mabiya darikar Sunni guda uku, wato Bahrain, Sudan da Daular kasashen Larabawa suka goyi bayan kasar Saudi Arabiya na yanke huldar jakadanci tsakanin su da Iran, abin da ya kara dagule yanayin da ake ciki a yankin.(Fatimah Jibril)