in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta kammala aikin kawar da na'urar tace sinadarin Uranium da ke Arak
2016-01-15 10:50:45 cri
Rahotanni daga Iran na cewa, yanzu haka an shiga matakin karshe na kawar da na'urar tace sinadarin Uranium dake Arak, kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar da aka daddale game da shirin nukiliya na Iran. Nan gaba kadan ne kuma ake sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA za ta gudanar da bincike game da lamarin.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya ce, idan har Iran ta aiwata da yarjejeniyar da aka daddale game da batun nukiliyar kasar yadda ya kamata, to kasar Amurka ma za ta cika alkawarin da ta dauka kwana nan, cikinsu har da soke takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa Iran.

A ranar 14 ga wanan wata ne, hukumar kungiyar EU ta bayyana cewa, idan IAEA ta tabbatar da cewa, Iran ta cika alkawarin da ta dauka na aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma daga duk fannoni, kungiyar EU za ta soke dukkan takunkumin da ta kakabawa Iran. Mataimakiyar shugaban hukumar kungiyar EU kuma wakiliyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro Frederica Mogherini ta ce, nan ba da dadewa ba za a aiwatar da yarjejeniyar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China