Jaridar Arab ta fidda rahoton cewa, daga cikin wadannan 'yan kasar Iran guda hudu, ana zargin uku daga cikinsu cewar sun aikata lafuffukan ta'addanci a kasar Saudi Arabiya, yayin da dayan ya aikata laifin leken asirin kasar ga sashin leken asiri na kasar Iran.
Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, ban da wadannan 'yan kasar Iran guda hudu, an kuma yanke hukunci na dauri wani dan kasar Iran a gidan kurkuku na tsawon shekaru 13, bisa zargin cewar ya nemi matasan kasar da su shiga cikin yake-yaken da ake yi a kasashen waje, kana bayan shekaru 13 da zai kasance cikin gidan kurkuku, Saudia za ta kore shi.
A makon da ya gabata ne 2 ga wata da dare, 'yan kasar Iran da dama suka taru a gaban ofishin jakadancin kasar Saudi Arabiya dake babban birnin kasar Iran, Teheran, inda suka saka wuta da kuma kai farmaki ga ofishin, sabo da kashe wani babban malamin Shi'a Sheikh Nimr Baqr al-Nimr da kasar Saudi Arabiya ta yi a wannan rana. Sa'an nan a kashegari kuma, kasar Saudi Arabiya ta sanar da yanke huldar diflomasiyyar tsakaninta da kasar Iran, lamarin da ya haifar da illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)